Labari Mai Dadi: Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’addan ISWAP 5, Sun Kwato Makamai Da Dama A Borno

FB IMG 1748102102600

Daga Aminu Bala Madobi

Dakarun sojojin Najeriya na Operation HADIN KAI sun yi nasarar dakile wani harin ta’addanci da kungiyar ISWAP  suka kai wa sansanin sojojin Najeriya a kauyen Gajibo da ke karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.

A cewar Zagàzola makama, ‘yan ta’addan sun kai hari kauyen Gajibo ne da misalin karfe 10:20 na daren ranar alhamis, inda sojojin rundunar ta 134 suka isa garin, wanda ya haifar da sake mamaye sansanin daga dakarun sojan.

A yayin farmakin, an kashe ‘yan ta’adda akalla 5 tare da kwato tarin makamai da harsasai da suka hada da bindiga kirar AK 101 guda daya, akwati daya mai dauke da alburusai 13 masu nau’in 5.56mm na NATO, harsashi na musamman 51 masu nau’in 7.62mm, da harsashi 16 nau’in 5.56mm na NATO.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *