Gwamnatin Amurka Ta Haramtawa Jami’ar Harvard Baiwa ‘Yan Najeriya Gurbin Karatu.

IMG 20250523 WA0531

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Shugaba Donald Trump ta haramtawa jami’ar Harvard baiwa daliban Najeriya da sauran kasashen duniya gurbin karatu a Jami’ar.

Ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta sanar da cewa an soke ikon Harvard na baiwa daliban kasashen waje gurbin karatu.

“Harvard ba za ta iya sake yin rajistar ɗaliban ƙasashen waje ba kuma ɗaliban ƙasashen waje dole ne su canza ko rasa matsayinsu na doka,” in ji sashen

Jami’ar Harvard dai ta fuskanci cece-kuce akan kudade da gwamnatin Trump, sakamakon kin biyan bukatun shugaban kasar da makarantar ta yi.

Trump ya bukaci malaman jami’o’in dasu bunciki laifin satar bayanai da kuma bayar da rahoton daliban kasa da kasa da ake zargi da rashin da’a.

Har ila yau Harvard ta bijirewa wannan umarni da Shugaba Trump ya gindaya

A wani bangare na sakamakon, gwamnatin Trump ta dakatar da dala biliyan 2.2 na tallafi da ta ke baiwa Jami’ar Harvard a watan da ya gabata.

A farkon wannan watan, sashen ilimi ya yi barazanar cewa Jami’ar Harvard ba zata sake samun tallafin gudanar da bincike ba.

“Wannan ya zama gargadi ga dukkan jami’o’i da cibiyoyin ilimi a fadin kasar,” in ji Kristi Noem, sakataren ma’aikatar tsaron cikin gida bayan yanke shawarar.

Saidai Jami’ar Harvard tayi kira da a soke matakin “haramtacce”

“Mun himmatu don cigaba da bada gurbin karatu tareda kiyaye ikon Harvard don karbar bakuncin ɗalibanmu da malamanmu na duniya, waɗanda suka fito daga ƙasashe sama da 140 – ”in ji jami’ar a cikin wata sanarwa.

“Wannan mataki na ramuwar gayya na barazana ga kafatanin al’ummar Harvard da kasarmu kuma yana lalata manufar ilimi da bincike na Harvard.”

A cikin shekaru goma da suka gabata, Harvard na ci gaba da samun karuwar ɗaliban ƙasashen duniya.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *