Tufka Da Warwara: Hukumar tace fina-finai ta janye dakatarwar da ta yi na haska wasu finafinai 22 a jihar Kano

FB IMG 1747755070738

Hukumar tace finafinai da dab i ta tamince da ci gaba da haska fina-finan da ta dakatar a masana’antar Kannywood domin kada masu samar da su, su tafka asara.

A wata sanarwa da kungiyar masu shirya fina-finai ta jihar Kano MOPPAN karkashin shugabanta Ado Ahmad gidan Dabino ta fitar ta ce sun yi zama da shugabannin hukumar tace fina finan ta jihar Kano.

Sanarwar ta ruwaito cewa, matsayar da aka cimma ta hada da ci gaba da haska fina finan da aka dakatar, tare da bayar da wa’adin mako guda ga masu shirya fina finan su mika duk wani shirin su a gaban hukumar domin tantancewa.

Idan zaku iya tunawa kwanaki 2 da suka gabata shugaban hukumar Abba El Mustafa ya fitar da. Sanarwar soke haska fina-finai, wanda hakan ya janyo cece kuce a masana antar.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *