EFCC Ta Mika Gidaje 753 da Aka Kwato daga Tsohon Gwamnan CBN

FB IMG 1747755599057

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mista Olanipekun Olukoyede, ya mika kadarori masu yawa da suka hada da gidaje 753 na zamani ga Ma’aikatar Gidaje da Ci gaban Birane, bayan an kwato su daga tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, yana mai bayyana cewa za a siyar da gidajen ne ta hanyar da ta dace da gaskiya da adalci, kuma za a gudanar da tsarin siyarwar ne ta hanyar Renewed Hope Portal.

“Yau na karɓi bakuncin Shugaban EFCC mai kwazo, Mista Olanipekun Olukoyede, wanda ya mika mana rukunin gidaje guda 753 da sauran dakunan zama da aka kwato, waɗanda ke cikin yankin Cadastral Zone na Babban Birnin Tarayya (FCT),” in ji Ministan.

Dangiwa ya bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin umarnin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar, cewa duk kadarorin da aka kwato daga hannun baragurbin masu rike da madafun iko su koma hannun gwamnati tare da amfani da su don amfanar da ‘yan kasa.

A ƙarshe, ya bayyana cewa dukkanin gidajen za a siyar da su ta hanyar tsarin saye da ke bayyane, wanda za a tallata shi sosai kuma za a tafiyar da shi ta hanyar Renewed Hope Portal, domin ba kowa damar shiga bisa gaskiya da adalci.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *