Kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida Manjo Janaral Muhammad Inuwa Idiris mai ritaya ya ajiye aikinsa na a daren Talata.
Wata takarda da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar yace gwamna Yusuf ya kadu da ajiye aikin da kwamishinan nasa yayi
Ya kuma mika sakon godiya sosai abisa gudun mowar da ya bayar.
Tuni gwamna Yusuf ya karbi takardar ajiye aikin na kwamishinan tsaron nan take.
Sai dai har zuwa hada wannan rahotan kwamishinan bai bayyana dalilansa na ajiye aikin nasa ba.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD