Da sanyi asubahin ranar Alhamis, 22 ga watan Agusta, 2024, wata motar dakon giya ta fada gefen gabar kogin Kano, dake garin Chalawa dake kan hanyar zuwa Madobi, karamar hukumar Kumbotso, a jihar Kano.
Lamarin dai ya faru ne a lokacin da direban motar giyar, yake kokarin ya juya akalar motar domin ya koma idan ya fito, ganin cewa ya makara har gari ya waye bai isa gurin da zai sauke barasar da ya ɗauko ba.
A zantawar wakilinmu da wani shedar ganin da ido kuma ma’aikacin hukumar Hisbah ta jihar Kano, a reshen hukumar dake karamar hukumar Kumbotso, mai suna Dahiru Saleh Chalawa, ya bayyana cewa, “da sanyin safiyar Alhamis dinnan ne, aka kira mu inda aka ce, mu zo ga wata babbar mota ta fada rami a gefen gabar kogi, kuma ana zaton motar giya ce,”
“Koda muku zo gurin kuwa, sai muka tabbatar ashe motar giya ta ɗauko, kuma kafin mu karaso wajen har direban motar ya yi kokarin kirawo dakarun hukumar kare faruwa hadari ta ƙasa (FRSC), don su kawo musu ɗauki.”
To sai dai yanzu haka direban motar giyar da yaransa, sun cika wandonsu da iska inda suka tsere.
A halin yanzu dai jami’an hukumar Hisbah ta jihar Kano, sun yi dirar mikiya a gurin da lamarin ya faru.

Al-Manasik Reporters
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj