Kotu a Faransa ta kwace jiragen fadar shugaban kasar Nijeriya guda 3

Screenshot 20240816 002350 Facebook

Wata kotu a kasar Faransa ta bada umarnin kwace jiragen fadar shugaban kasa guda 3.

Financial Times ta wallaf cewa jiragen da kotun ta bada umarnin kwacewa sun hada da kirar Falcon 7X da Boeing 737-7N6/BBJ da Airbus A 330-243 wadanda aka ajiye a filin tashi da saukar jirage na birnin Paris.

Kotun ta bada umarnin ne bayan wani kamfanin kasar China mai suna Zhongshan ya shigar da kara kan soke kwangilar da gwamnatin jihar Ogun ta bashi a 2016.

Hukuncin na kotun dai shi ne na baya bayan nan da wani kamfanin kasar Waje ya shigar da Nijeriya.

A shekarar 2013 dai kamfanin da gwamnatin Ogun suka sanya hannu kan yarjejeniyar samar da rukunin masana’antu.

Kamfanin, acewar yarjejeniyar shi ne zai mallaki kaso 60 kamar yadda tanadin yarjejeniyar ya nuna.

Daily Trust.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *