An yanke wa sojoji 24 da suka yi yunkurin juyin mulki a kasar Saliyo hukuncin zaman gidan wakafi ciki har da na daurin shekaru 120, bayan kotun sojojin kasar ta same su da hannu a yunkurin kifar da gwamnati.
Alfijir labarai ta ruwaito rahotanni daga birnin Freetown na cewa alkalai bakwai da suka jagoranci zaman kotun sun tabbatar da hukuncin dauri na dogon zango ga sojojin bayan shafe kusan watanni takwas ana gudanar da shari’a kan zargin hannunsu a kifar da gwamnatin shugaba Julius Maada Bio a watan Nuwambar 2023.
A yayin arangamar sojojin sun bude wuta a babban birnin tare da kutsawa fadar shugaban kasa da barikin soji da kuma babban gidan yarin birnin Freetown inda fursunoni sama 2000 suka tsere.
Hukumomi a wancan lokacin sun tabbatar da cafke mutune sama da 80 da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin, ciki har da tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma, wanda daga bisani kotu ta sallame shi bisa dalilan rashin lafiya.
DW
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj