Daga Aminu Bala Madobi
Dan majalisar tarayya daga Kano mai wakiltar Sumaila -Takai ya yi barazanar gurfanar da jaridar Legit kan abin da ta wallafa na batanci batare da sanin ba.
Alfijir labarai ta ruwaito ita dai kafar labarai ta Legit, Gidan jarida ne mamallaka jaridar Legit Hausa dake wallafa labaran turanci da Hausa na yanar gizo da sauran kafafen sada zumunta.
Dan majalisar wakilan Hon. Rabiu Yusuf, ya yi barazanar shigar da kamfanin kara sakamakon wallafa rubutu dake alakanta Dan majalisar da neman amincewar majalisar wakilai kan auren jinsi da madigo.
Dan majalisar, a wata wasika da lauyoyinsa, Messrs. Ahmad Musa & Co, suka aikewa mawallafin jaridar ranar Juma’a, ya yi ikirarin cewa wata jarida ta wallafa rubutu ta hanyar bata sunan sa a wannan rana.
A cewar wasiƙar, mai taken BUKATAR NEMAN RUBUTUN AFUWA TARE DA JANYE KALAMAN BATANCI AKAN BARR. RABIU YUSUF (Dan Majalisar Wakilai), Mai taken Auren Jinsi: Dan Majalisar Kano Na Neman Najeriya Ta Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Samoa.
A wasikar wanda Yusuf A. Faragai ya sanyawa hannu, wadda kwafin jaridar Nigerian Sketch ta gani, ta ce “An wallafa abin ne da gangan domin bata sunan abokin huldar mu ga alummar da yake jagoranta…”, inda ya kara da cewa “… abin da kuka wallafa na batanci ya kai matuka wajan taba kima, kwarjini, mutunci da farin jinin wanda muke wakilta a idon jama’arsa, mutanen jihar Kano da Najeriya baki daya.”
Yadda Batun Yake…
Hon. Rabiu Yusuf shi ne shugaban kwamitin kula da yarjejeniyoyi, ka’idoji a majalisar wakilai, Da yake jawabi a ranar Alhamis yayin wani taron yanar gizo da cibiyar kirkire-kirkire da raya kasa (CJID) ta shirya kan batun shigar Najeriya cikin yarjejeniyar Samoa, ya lura cewa yarjejeniyar nada dan fa’ida da fa’idodi ta wasu bangare ga kasar.
Sai dai ya jaddada muhimmancin cire wasu tanade-tanade da ba su dace da dabi’u da al’adu da addinai na Najeriya ba.
Ya kara da cewa yarjejeniyar aba ce mai wahala da ya kamata a tattauna a kai a kokarin fito da kimar kasar.
“Akwai haɗari amma zamu iya sanya sharadi irin na cikin gida. Tsoron shine an ba shi suna cikin hikima da sigar wayo wato (LGBTQ). Ba ma bukatar sa kwata-kwata domin hakan ya saba wa dokokinmu.”
Sai dai kuma babban labarin da jaridar Legit ta fitar.
LGBTQ wani lamari ne mai cike da sarkakiya a yawancin kasashen Afirka da suke kallon lamarin a matsayin rashin da’a kuma ya saba wa al’adu da addininsu. Wasu kasashen Afirka sun haramta shi kai tsaye, yayin da wasu ke da tsauraran dokoki da ka iya zama aiwatar dashi, doka ce datayi daidai da matsayin hukuncin kisa.
Saboda wasu dalilai duk da haka kasashen yammacin duniya na ci gaba da chuso tsarin ko ta halin-kaka zuwa kasashen Afirka, suna ba da tallafi ga ƙungiyoyin da ke tallata ta da kuma ba da gudummawar shawarwari don tabbatar da shi.
Yarjejeniyar Samoa
Yarjejeniyar Samoa hadin gwiwa ce tsakanin kasashe mambobin kungiyar Afirka, Caribbean, da Pacific (OACPS) da Tarayyar Turai (EU).
Yarjejeniyar wacce ta bayyana dangantakar tattalin arziki da kasuwanci ta kungiyar tarayyar turai EU da kasashe 79 (47 daga Afirka, 16 a yankin Caribbean da 15 a yankin tekun Pasifik da Jamhuriyar Maldives), ta tanadi fannoni shida da suka fi ba da fifiko wajen tunkarar kalubalen duniya (dimokradiyya, daidaiton jinsi da haƙƙin ɗan adam, haɓakar tattalin arziki da ci gaba mai dorewa, sauyin yanayi, ci gaban ɗan adam da zamantakewa, zaman lafiya da tsaro).
Abin Damuwar Ga Najeriya
Najeriya tayi fatali daga rattaba hannu kan yarjejeniyar a watan Nuwambar bara bayan da wasu kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin suka nuna damuwa game da sashe na 9 na yarjejeniyar, wanda ya ce “ mutunta ‘yancin dan Adam, ka’idojin dimokuradiyya, da bin doka da oda…
Kungiyoyin sun ce wannan kawancen wani shiri ne na ‘yan madigo, da ‘yan luwadi, da masu canza jinsi, da kuma ‘yan luwadi (LGBTQ) a cikin kasar, wanda suka ce Najeriya ba ta cikin irin wannan kasashe dake shaawar shiga.
Bukatar Rabiu Yusuf
Lauyoyin dan majalisar sun bayyana cewa, rubutun da jaridar Legit ta wallafa, sun tafka ta’asa ta hanyar wallafa rubutu da sunan sa, Wanda wannan ba ra’ayin sa bane, ra’ayin su ne, Adan haka yana neman gidan jaridar da gaggawa cikin awanni 24 dasu fito su nemi yafiya kuma su wallafa a manyan jaridu 2 da kuma dandalin sada zumunta.
A cewar lauyoyin Dan majalisar rashin bin wannan bukatun nasu zai sa a shigar da gidan jaridar kara gaban kuliya kan mawallafin jaridar Legit Hausa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj