Gwamnatin Najeriya Ta Sanya Ranar Bude Shafin Baiwa Dalibai Rancen Kudi A Watan Nan Da Muke Ciki

ALFIJIR 1

Tinubu ya kuma ba da umarnin a saka ’yan Najeriya da suka cancanta da ke da ilimin boko da kuma wadanda ke jami’o’i masu zaman kansu a cikin shirin.

Alfijir labarai ta ruwaito shugaba Tinubu zai kaddamar da shirin bayar da lamuni na dalibai da ake jira a hukumance a Abuja ranar 21 ga watan Fabrairu.

Tsarin  lamunin ya dogara ne ga duk ɗaliban Najeriya a manyan makarantun Nijeriya tare da tsarin biyan kuɗi mai sauƙi wanda zai fara daga shekaru biyu na samun aikin hidimar ƙasa.

Tinubu ya kuma ba da umarnin a saka ’yan Najeriya da suka cancanta da ke da ilimin boko da kuma wadanda ke jami’o’i masu zaman kansu a cikin shirin.

Daliban da a halin yanzu suka shiga jami’o’i ne kawai za a ba su kashi na farko na shirin kamar yanda Jaridar TheCable ta wallafa.

Mr. Akintunde Sawyerr, sakataren zartarwa na Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya (NELFUND), ya tabbatar da ranar kaddamar da shirin.

Dangane da ka’idojin zaɓe, mai nema dole ne ya zama ɗan Najeriya kuma dole ne ya kasance ɗalibi na gaskiya a manyan makarantun ilimi a Najeriya.

Yayin Tsarin  za a bukaci masu nema da su samar da muhimman bayanan sirri kamar lambar NIN BVN da lambar JAMB

Za a bayar da lamunin ne kai tsaye ga makarantun ta hanyar asusun ajiyar kudi na NELFUND da ke babban bankin Najeriya CBN ba tare da wani mai shiga tsakani ba.

kwamitin na musamman na NELFUND za su hada da  gwamnan babban bankin kasa CBN a matsayin shugaba; babban sakataren NELFUND a matsayin sakatare; wakilin ministan ilimi; da kuma shugaban hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC).

Sauran su ne: wakilin dandalin mataimakan shugabannin jami’o’in Najeriya; Wakilin taron shugabanni na dukkan makarantun kimiyya da fasaha na Najeriya na dukkan kwalejojin ilimi a Najeriya; wakilin ministan kudi, babban mai binciken kudi na tarayya; wakilin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC; wakilin kungiyar lauyoyin Najeriya NBA da kuma wakilin kungiyar malaman jami’o’i ASUU.

Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da dokar lamunin Dalibai (Access to Higher Education) a shekarar 2023 don samar da sauki ga ‘yan Najeriya masu karamin karfi ta hanyar lamuni mara ruwa, kuma Tinubu ne ya sanya wa hannu a ranar 13 ga Yuni, 2023.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *