EFCC ta kama shugabanin Zenith, Jaiz, Bank bisa zargin damfarar Edu da Sadiya-Farouq

FB IMG 1704870772714

Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta damke shugabannin manyan bankunan Zenith, Providus, da Jaiz bisa zargin almubazzaranci da almundahana da ake alakantawa da abin kunyan ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu da magabacinta Sadiya Umar. – Faruk.

Alfijir labarai ta rawaito wasu majiya masu tushe daga fadar shugaban kasa ta shaidawa Peoples Gazette a ranar Talatar da ta gabata cewa shugabannin bankunan da ake bin diddigin su tun bayan da jama’a suka yi ta cece-kuce kan yadda ake karkatar da kudaden al’umma zuwa wasu asusu na sirri, yanzu haka suna hannun EFCC.

A halin yanzu dai hukumar EFCC na bin diddigin wasu makudan kudaden gwamnati da aka tura zuwa asusun wasu masu zaman kansu, matakin da Edu da Farouq suka amince da su.

Ms Farouq, wacce ta jagoranci ma’aikatar jin kai, magance bala’o’i da ci gaban al’umma a gwamnatin da ta shude, ana kuma gudanar da bincike a kan almundahanar akalla Naira biliyan 37 na kudaden al’umma da aka ware domin shirin mika sharadin mika kudi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na lokacin.

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya kaucewa binciken lamarin.

A halin da ake ciki, Ms Edu ta ce bata da hannun cikin badakalar, kuma ta kuduri aniyar yaki da cin hanci da rashawa a yayin da ake ta cece-kuce kan bukatar da ta yi ba bisa ka’ida ba na aika kudi zuwa wani asusu na sirri.

Ms Edu ta bayyana hakan ne a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook ga wadanda suka ci gajiyar Npower.

“Ya ku ‘yan uwa masu amfana da Npower, ina so in tabbatar muku da ku kwantar da hankulan ku a cikin zarge-zargen da kuma dakatarwar da nake fuskanta. Zuciyata da hannayena suna da tsabta, kuma na himmatu wajen yaki da cin hanci da rashawa,” in ji Ms Edu.

Ta kara da cewa, “Yana da mahimmanci a sani cewa wasu mutane masu mugun nufi na iya amfani da ikon gwamnati a kan ku. Ku kasance cikin karfin Zuciya, Nan ba da dadewa ba za mu shawo kan waɗannan ƙalubalen. “

An dai gudanar da bincike-binciken almundahana da dama tun lokacin da shugaban kasa Bola Tinubu ya hau kan karagar mulki, lamarin da ya sa ake tsare da manyan mutane kamar gwamnan CBN Godwin Emefiele da shugaban EFCC Rasheed Bawa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *