Shugaba Tinubu ya tsige wasu shugannin ma’aikatu 2

IMG 20231231 103804

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tsige wasu manyan hadiman gwamnatin tarayya waɗanda magabacinsa, Muhammadu Buhari ya naɗa.

Alfijir labarai ta rawaito Shugaban Najeria Bola Tinubu ya kori shugaban hukumar FCCPC (Federal Competition and Consumer Protection Commission), Babat da darakta janar kuma shugaban hukumar BPE (Bureau of Public Enterprises), Alexander Ayoola Okoh.

Wannan mataki na tsige shugabannin hukumomin biyu na kunshe ne a wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasa, ranar Litinin, 8 ga watan Janairu.

Bayo Onanuga, babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru ya wallafa sanarwan a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Sanarwan ta umarci waɗanda matakin ya shafa su miƙa harkokin mulki ga babban ma’aikacin da ke ƙasa da su a hukumomin yayin da korarsu ta fara aiki nan take.

Manyan ma’aikatan da zasu miƙa wa ragamar hukumomin za su ci gaba da kula da harkokin waɗannan hukumomin har zuwa lokacin da shugaban ƙasa ya naɗa sabbi.

Sanarwan mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ta ce:

“Ana umurtan korarrun shugabannin hukumomi su miƙa ragama ga manyan jami’an gwamnati da ke ƙasa da su a wurin gabanin naɗa waɗanda zasu maye gurbinsu.”

Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan shugaba Tinubu ya dakatar da ministar harkokin jin ƙai da walwala, Dokta Betta Edu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *