โYan sanda sun tsare Daraktan Maโaikatar Ruwa ta Kano kan zargin karkatar da injinan rarraba ruwan sha a jihar.
Alfijir labarai ta rawaito Abubakar Gambo ya shiga hannun โyan sanda ne tare da wasu mutane biyu kan zargin su da yin takardun bogi na smaun izinin yi gwanjon wasu manyan injinan rarraba ruwan sha da kuma tankuna.
Kwamishinan โan sandan jihar, Hussaini Muhammad Gumel, ya ce mutanen sun shiga hannun ne bayan Kwamishinan Ruwa na jihar, Ali Makoda, ya musanta ba da izinin sayar da injinna ruwan da kuma tankuna, yana mai cewa tsantar damfara ce suka shirya.
CP ya kara da cewa rundunarsa na ci gaba da bincike kan lamarin domin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya.
Sauran wadanda aka kama su ne Mataimakin Sakataren Gudanarwa, Baba Yahaya da kuma Nuhu Mansir, wanda tsohon Manajna Shirin Noman Rani a KAREFA ne a Karamar Hukumar Tudun Wada.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐๐
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp