Gwamnatin Kano ta Bayyana Dalilanta na Ciyo Bashin Naira Miliyan Dubu 4

FB IMG 1696417537151 edit 786631287899

Gwamnatin jihar Kano tace za ta ciyo bashin Naira Miliya dubu hudu domin gudanar da aikin samar da wutar lantarki a fadin jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan ta cikin wata Wasika da ya aikewa Majalisar inda ya bukaci majalisar ta sahale masa ya ciyo bashin.

Gwamnatin tace idan Majalisar dokokin jihar Kano ta amince mata ta ciyo bashin to zata yi amfani da kudin ne don gudanar da aikin samar da wutar lantarki a jihar.

Da yake yiwa Majalisar karin haske, shugaban masu rinjaye na Majalisar, kuma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala Lawan Hussaini Chediyar yan gurasa Dan Majalisa ya ce bashin zai taimaka wajen cigaban Kano.

“Babban bankin Nigeria CBN zai bayar da bashi wanda babu kudin ruwa a cikinsa kuma matukar aika ciyo bashin zai taimaka wajen samar da ingantacciyar wutar lantarkin wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci da tsaron Kano” .a cewar Dan majalisar na Dala

Lawan Hussaini ya kuma roki yan Majalisar da su hada kai domin amincewa gwamnatin don ta ciyo bashin.

“Ka’idoji uku ne za’a cika kafin karbar bashin daga CBN kuma ka’idojin sun hadar da Amincewar Gwamnan Kano da Majalisar zartarwa ta jiha da kuma Amincewar Majalisar dokoki ta jiha,” inji Lawan Hussaini.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *