Daga Baba Usman Gama
Babban Sifeton ‘yan sanda ya bayar da umarnin wajibcin yi wa masu raunin harbin bindiga aiki, ba tare da jiran rahoton ‘yan sanda ba.
‘Yan sanda sun kama matashi kan zargin kashe wata mata mai ‘ya’ya takwas a Gombe.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana cewa mutane da dama sun raina shi a lokacin da ya karba ragamar mulki saboda kwarewarsa a harkar rawa.
’Yan Shi’a sun yi tattakin goyon bayan Falasdinawa a Abuja.
Mashahurin Attajiri Femi Otedola ya yi kyautar naira miliyan daya ga kowani dalibin Jami’ar Augustine dake Ilara-Epe a jihar Legas.
Ƴan bindiga sun sake shiga wani rukunin gidaje a yankin Kubwa a birnin tarayya Abuja, sun sace mutane uku a cikin dare.
Za a yi wa ’yan mata miliyan 7 rigakafin cutar kansar mahaifa a Najeriya.
Hatsarin jirgin ruwa ya halaka mutane 2, wasu huɗu sun jikkata a jihar Legas.
Kotun ƙararrakin zaɓe a Sokoto ta tabbatar da nasarar sanata Aliyu Wamakko na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen sanatan Sokoto ta Arewa.
Kotun Majistare a Legas ta umarci ɗan tireda da ya saci damin Albasa share harabar Kotu na awa 20.
‘Yan sanda sun kama daruruwan Yahudawa a birnin New York na Amurka bayan zanga-zanga a babban zauren tashar jiragen kasa ta Grand Central don kyamar hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza.
Shugaban lardin Gauteng na Afirka ta Kudu, ya yi kira a koma tsarin takaita ta’ammali da tsabar kudi don rage yawaitar fashi da makamin da ake fuskanta.
An fara gwajin allurar tsarin iyali ta maza a Indiya.
Babban Zauren MDD ya kada kuri’ar neman tsagaita wuta nan take a Gaza.
EPL: Tottenham ta sami nasara akan Crystal Palace da ci 2:1 a wasan jiya.
Laliga: Girona ta sami nasara akan Celta Vigo da ci 1:0 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ