Ana sanar da jama’a cewa In Sha Allah ranar Alhamis za’a rufe gadar sama ta kofar Nassarawa zuwa gidan gwamnati, da kuma ta Obasanjo saboda wasu ayyuka da za a yi a gadojin.
Saboda haka ake sake tunatar da al’ummar jihar Kano musamman masu bin wannan hanya cewa za’a rufe wadannan gadoji, sannan kuma za’a bude hanyar kasa saboda kulle saman na dan wani lokaci da za’a yi.
Muna godiya bisa goyon baya da al’ummar jihar Kano ke bamu a ko da yaushe.
ALLAH Ya taimaki jihar Kano da kuma gwamnan Kano Engr Abba K. Yusuf.
Sanarwa:
Engr Marwan Ahmad
Kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo