Manyan ‘yan siyasa da ke adawa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio na shirin tsige shi a yayin zaman da majalisar za ta yi, idan ta koma aiki bayan hutun da suka tafi a ƙarshen wannan watan.
Alfijir Labarai ta rawaito rahotanni sun nuna cewa Sanatocin sun ji haushin yadda tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom ya zama ɗan amshin Shata ga Shugaba Tinubu maimakon biyan buƙatun ‘yan majalisar da ‘yan Najeriya baki ɗaya.

Sun yi zargin cewa kusancin da ke tsakanin Akpabio da Shugaban ƙasar ya sa ba ya mai da hankali ga abokan aikin sa, da kuma yin aiki tukuru domin cimma burin ‘yan Najeriya duk da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa wasu daga cikin Sanatocin da suka fusata da shugaban majalissar akwai wasu tsaffin gwamnonin Arewa maso yamma guda biyu, in da suke son yin amfani sakon kwanan nan da Akpabio ya saki, inda yace “an aika da addu’o’i a akwatunan wasikunsu domin yin bukukuwan Hutu” sun ce domin hukunta shi.
Wata majiya mai tushe a majalisar da ta san shirin da ake ƙullawa ta ce tuni kungiyar ta ƙin goyon bayan Akpabio ta gudanar da tarurruka da dama a Saudiyya da Ilorin domin kammala shirye-shiryen tsige shi idan Majalisar ta dawo daga hutu.
Babban majiyar NASS ta ce “Daga cikin laifukan da Sanata Akpabio ya yi akwai zargin da ake yi masa na tsananta alaka da Shugaba Bola Tinubu.
Har ila yau, suɓul da bakan da Shugaban Majalisar Dattawa ya yi a ranar da za a dage zaman zuwa hutu, sun ce shi za su riƙe a matsayin makamin da za su yaƙe shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb