Maryam Shetty na cikin matasan jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya da suka taka rawa a zaben 2023.
Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya janye Maryam Shetty daga cikin mutanen da ya mika sunayensu ga ‘yan majalisar dattawan kasar domin ya nada su ministoci.
Shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a zaman da majalisar ta yi ranar Juma’a.
Ya ce Shugaba Tinubu ya tura musu sunan Dr. Mariya Mairiga Mahmoud Bunkure don maye gurbin Maryam Shetty.
Mariya Mahmoud Bunkure tsohuwar Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi ce a gwamnatin tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Hakazalika shugaban majalisar dattawan ya ce an mika musu sunan fitaccen lauyan nan Festus Keyamo domin a nada shi minista.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI
Very interesting and like to be one of you member that receive news always. Tnx