Tinubu Ya Nemi Majalisar Dattijai Ta Amince Da Tura Rundunonin Sojoji Kasar Niger

Shugaban kasa Bola Ahamed Tinubu ya aikewa majalisar dattijai shirinsa na aike da rundunonin sojoji Niger domin murkushe wadan da sukai juyin mulki.

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban majalisar datijai Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar da Tinubun ya aike da ita ranar juma’a.

Wani bangare na wasikar yace” Sakamakon yanayi mara dadi da kasar nijar take ciki, bayan juyin mulki da sojoji sukai, kungiyar ECOWAS a karkashin mulkina tayi alla wadai da wannan juyin mulkin.”

“ECOWAS ta kuma dau tsauraren matakai akan kasar ta Nijar, sanan kuma zamu tura rundunar sojoji kasar domin tabbatar da zaman lafiya da kuma dawo da demokradiya” Inji Wani bangare na wasikar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

3 Replies to “Tinubu Ya Nemi Majalisar Dattijai Ta Amince Da Tura Rundunonin Sojoji Kasar Niger

  1. It doesn’t make sense. At this difficult time Nigeria to attack another country because of poli.

  2. As salam aleykum
    Wanan magana ta shugaba Ahmed bolo tunubu ba komay bace face yanada wata manufa game da kasar Niger bama fatan hakan yakasance amma saboda munada alaka atsakaninmu mu mutanan Niger da mutanan Nigeria to shugaba Ahmed bolo tunubu yanaso yakawo karshen alakarnan kar ya Manta muda iyaka da kasar Nigeria ta sama da kilomètre dubu da doria wanan hari ba iyya birni yamay ba kadey tse tsaya xe gama kasar gabakidaya soboda idan akayi harbiy ankashe bazoum saboda bayada za ayyi abarshi daray Kuma xe shafi kasar baki daya xe shafi kuma en Nigeria dake baki iyakar Niger da Nigeria

  3. Daman a Nigeria muna da sojojin da zasukai dauki wata kasa Amma Yan taadda sukecin karensu Babu babbaka ayankin arewacin Nigeria? Allah Ya kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *