Gwamnatin sojin Nijar ta katse huldar diflomasiyya da Najeriya, Togo, Amurka da kuma ta fuskar tsaro da tsohuwar uwargijiyar kasarsu Faransa.
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin sojin Nijar din ta kuma ki ganawa da wakilan da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), ta tura domin tattaunawa da ita.
Wani daga cikin wakilan ya shada da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kasa da awa 24 da isarsu birnin Yamai suka baro kasar Nijar, “ko kwana ba mu yi ba,” ballantana ganawa da Janar Abdourahamane Tiani kamar yadda aka tsara.
A ranar Laraba ne ECOWAS ta tura wakilan nata, karkashin jagorancin tsohon shugaban mulki sojin Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, domin tattaunawa da gwamnatin sojin da ta yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki.
Da farko dai gwamnatin Najeriya ta sanar cewa kwamitin na Abdulsalami Abubakar zai gana da Janar Tiani inda zai gabatar wa gwamnatin sojin da ta yi juyin mulki a Nijar bukatun ECOWAS.
Kungiyar wadda Shugaan Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu yake jagoranta, ta kakaba wa gwamnatin sojin ta Nijar takunkumin karya tattalin arziki, sannan a ranar Lahadi ta ba wa sojojin wa’adin mako guda su mika wa Bazoum mulkinsa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI
Kuwa yarike matsalar kasar sa abarsu suye abinda suka gadama susukasan matsalar kasarsu muma akwai matsala akasar dayawa amma suntafi wata dan neman suna da yankasar a bala i