Gwamnatin Tarayya za ta yi wa kan ta, jihohi da ƙananan hukumomi watandar Naira biliyan 907.
Alfijir Labarai ta rawaito hakan ya biyo bayan cire tallafin fetur da aka yi, har Gwamnatin Nijeriya ta tara Naira tiriliyan 1.9 a cikin watan Yuni.
Adadin yawan kuɗaɗen shiga da aka tara a cikin watan Yuni ya zarce yawan adadin waɗanda aka tara a watan Mayu, bilyan 786.161.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Bola Tinubu, Dele Alake ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Alhamis.
Ya kara da cewa daga cikin ragowar kuɗaɗen, za a killace Biliyan 790, sauran kuma a zabtare haraji a cikinsu.
Wannan kasafin da gwamnatin tarayya za ta yi, ya samo asali daga cire tallafin fetur da tayi a hawan shugaba Tinubu.
Yace ganin al’ummar kasar ta shiga raɗaɗin tsadar rayuwa, gwamnati za ta raba tallafi ga marasa galihu, domin rage musu raɗaɗin.
Yayin da aka fara shirye-shiryen raba tallafin, Majalisar Tsara Tattalin Arziki ta kasa, tace rajistar sunayen masu karɓar tallafi da ake dashi a baya ba sahihiya ba ce.
Majalisar ta ce Gwamnoni su fito da tsarin cikakkar rajistar marasa galihu, domin wadda ke amfani da ita ba sahihiya ba ce.
Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo ne ya yi wannan bayani, bayan tashi daga taron su a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Alhamis.
Ya kara da cewar ya dace tallafin da za a fara rabawa ya kasance yana isa ga marasa galihu.
“Ya kamata mu faɗa wa kan mu gaskiya cewa babu wata sahihiyar rajistar marasa galihu a faɗin ƙasar nan.”
Ya kuma yi bayani cewa Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni su fito da tsarin turawa marasa galihu alawus-alawus na rage tsadar rayuwa, gwargwadon karfin su.”
“Misali Gwamnonin da ba su biya kuɗaɗen famsho ba, su yi azamar biya, waɗanda ba su biya ariyas ba suma su fara amfani da kuɗaɗen tallafin su bayar.
Hakazalika “Gwamnoni su ma tilas su rage almubazzaranci, domin a halin yanzu babu wani dalilin da gwamna zai fita da tawagar motoci 20.
Premium Times Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb