Kotu Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya N2m Ga Mutanen Da Aka yi Yunkurin Rugujewa Gidaje

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta umurci gwamnatin jihar da sauran wadanda aka yi ƙara, su biya wasu mazauna unguwar Salanta, kudi naira miliyan ɗaya kowannensu akan yunƙurin rusa musu kadarori ba bisa ƙa’ida ba.

Alfijir Labarai ta rawaito Alkalin kotun, Mai shari’a Simon Amobeda ya yanke hukuncin cewa yunƙurin gwamnatin Kano da jami’anta na sanya wa gidan Saminu Shehu Muhd ​​da na Tasiu Shehu Muhd ​cikin ​jerin gidajen da za a iya rushewa bayan an buga musu lambar jan fenti ba tare da bin ƙa’ida ba, tauye ƴancinsu ne na mallakar kadara kamar yadda sashe na 43 da 44 na tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tabbatar musu.

A nasa bangaren Barista Bashir Ibrahim, wanda ya shigar da karar a madadin Saminu da Tasiu, bayan yanke hukuncin yana yaba wa kotun bisa wannan hukunci, inda ya bayyana hakan a matsayin wata alama ta kare haƙƙi da martaba ƙimar ɗan’adam.

A nasa bangaren, lauyan gwamnatin jihar Kano da sauran waɗanda aka yi ƙara a shari’ar, Barista Musa Dahuru Muhd ​​daraktan shari’a a ma’aikatar shari’a ta Kano ya ce za su yi nazari a kan hukuncin tare da bai wa gwamnati shawara game da mataki na gaba.

Solacebase

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

2 Replies to “Kotu Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya N2m Ga Mutanen Da Aka yi Yunkurin Rugujewa Gidaje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *