Alfijir Labarai ta rawaito Kungiyar Tsofaffin Daliban Makaranta Sakandare Gwale Aji Na 2004, Sun biyawa wasu ɗalibai marayu Kudin Jarrabawa Neco ta shekarar 2023, mutume 3.

Dir Ghali da Saifullahi da marayun
Directan makarantar Malam Ghali Mukhtar Bala ya yaba da wannan namijin kokarin da kuma kishin ilimi, da wannan tsaffin daliban yan aji na 2004 suka yi.
Bala ya kuma yi kira ga sauran takwarorinsu na makarantar fa kuma kano baki daya da suyi koyi da wannan kokarin don tallafawa al’umma baki daya.
A nasa bangaren Sakataren kungiyar daliban aji na na 2004 Saifullahi Shehu Ishaq ya ce wannan shine irin aikin da suka saka a gaba, wato taimakawa yan uwansu ɗalibai da malamansu da kuma ita kanta makarantar.
Shehu ya kuma yi kira da dalibai kan jajircewa wajen neman ilmi da kuma aiki da shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Allah ya Saka da Alkairi Ameen