An Rushe Shatale Talen Kofar Gidan Gwamnatin Kano

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin jihar kano a ci gaba da rushe-rushen inda tace an gina ba bisa ka’ida ba, gwamnatin ta rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnan jihar a daren jiya talata.

Sai dai har yanzu babu wani bayani da gwamnatin ta fitar a matsayin dalilin rushe shatale-talen.

Shatale-talen dai shi ne mafi kayatarwa cikin manyan shatale-tale da ake da su a fadin jihar kano.

Ko a baya anga yadda gwamnatin ta dinga rushe shi ana narka masu kudade masu yawa don kawata shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “An Rushe Shatale Talen Kofar Gidan Gwamnatin Kano”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *