Alfijir Labarai ta rawaito Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya kori kwamishina da wasu mataimaka biyu a ranar Talata
Gwamnan ya kori kwamishinan noma na jihar, David Apeh.
Haka kuma an kori mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin bada agajin gaggawa, Mista Danladi Isah-Yunusa, da Hajiya Maryam Salifu, shugabar hukumar kula da gidajen otel da yawon bude ido ta jihar Kogi.
Korar mutanen uku na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar, Misis Folashade Ayoade-Arike, ta fitar a Lokoja ranar Talata.
Ko da yake ba a bayar da dalilin korar Apeh ba, Ayoade-Arike ya ce gwamnan ya amince da dakatar da nadin nasa nan take.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ