Shugaba Buhari Shima Ya Roki Ƴan Najeriya Da Su Yafe Masa

Alfijr ta rawaito Shugaba Buhari ya roki ‘yan Najeriya da ya yi wa laifi su gafartawa masa, sannan kuma ya godewa ‘yan Najeriya da suka jure masa tsawon shekaru takwas da ya kwashe yana kan gadon mulki.

Da yake jawabi a lokacin da mazauna babban birnin tarayya, FCT, Abuja, suka kai masa gaisuwar Sallah, shugaba Buhari ya roki wadanda yayin gudanar da ayyukan sa na tsarin mulki ya cutar da su yafe masa.

Shugaban wanda ya ce yana kirga kwanakinsa ne wansa zai koma zuwa mahaifarsa ta Daura, ya kara da cewa gidansa na da nisan kilomita takwas zuwa Jamhuriyar Nijar.

Ya lura cewa ya samu duk abin da ya roki Allah ya bashi, kuma zai yi ritaya a gida.

Ya ce: “Na gode muku, Ina ganin kaina mai sa’a da na kasance gwamna, minista, shugaban kasa kuma yanzu na zama shugaban kasa na wa’adi biyu.”

Ya yaba wa mazauna babban birnin tarayya Abuja saboda kasancewa masu hakuri, ya kara da cewa. Da gangan na shirya in yi nisa da ku.

A yayin da ya ke zayyana yadda ya fadi zabe har sau uku har ya kare a kotun koli, ya ce fasaha ce ta hanyar katin zabe na dindindin, PVC ta kawo masa dauki a 2015.

Buhari an rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu, 2015 na tsawon shekaru hudu.

An sake zabe kuma ya sami nasara aka rantsar shi a ranar 29 ga Mayu, 2019 zuwa yanzu

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *