Alfijr ta rawaito ‘yan sanda biyar da ma’aurata sun rasa ransu, yayin da wasu ‘yan bindiga 5 a safiyar Juma’a a mahadar Okpala da ke karamar hukumar Ngor Okpala a jihar Imo suka kai musu hari.
Ma’auratan masu suna Mr da Mrs Chinaka Nwagu wadanda suka fito daga yankin Amankwo Okpala.
Rahotanni sun ce lamarin ya jefa mahadar tare da daukacin al’ummar yankin cikin firgici saboda ba zato ba tsammani hada hadar wajen ta zo karshe.
Wani ganau mai suna Uche kuma dan uwa ga ma’auratan ta shaidawa PUNCH cewa ‘yan sandan da aka kashe sun taso ne daga sashin ‘yan sanda da ke makwabtaka da Abo Mbaise domin cin abinci a mahadar.
Ya ce a yayin da ‘yan sandan ke cin abinci, wasu ‘yan bindigar suka tuka mota zuwa wurin inda suka bude musu wuta.
Ya ce yayin da aka harbe ‘yan sanda uku a wurin, wasu biyu kuma sun gudu zuwa wani shago da ke kusa da wurin, amma maharan sun garzaya zuwa shagon suka kashe su sannan suka kashe ma’auratan da ke da shagon da suka shiga.
Wani ganau ya bayyana cewa bayan kashe ‘yan sandan, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da bindigunsu guda biyar.
Majiyar ta ce, “Bakar Juma’a ce a cikin al’ummarmu.
Wannan abin takaici ne sosai. Al’ummar mu na zubar da jini.
Kowa ya rude. Ma’auratan sun ƙaura daga Legas kusan shekara ɗaya da ta wuce, mun ajiye gawarwakinsu a dakin ajiyar gawa, an rufe kasuwa mutane a nan sun gudu saboda kaduwa da tsoro
wannan abin rashin imani ne.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ