
Alfijr ta rawaito Babban Sakataren Yada Labarai na Shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ne ya shaida wa PUNCH a wata tattaunawa ta musamman a ranar Juma’a, 14 ga Afrilu, 2023.
A cewarsa, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta riga ta mika wa hukumar harakokin laifuka sama da 50 na laifukan zabe.
“Hukumar ta karbi takardun kararraki sama da 50 daga hukumomin ‘yan sanda.
Ya kara da cewa akwai sama da mutane 200 da ake tuhuma da za a gurfanar da su gaban kuliya.
“Hukumar ta umurci ma’aikatar shari’ar ta da ta yi nazarin bayanan tare da ba ta shawara a kan masu gabatar da kara.
Tuni dai sashen ya fara aiki kuma da zarar ya kammala za ta koma hukumar bisa ga haka,” inji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ