
Alfijr ta rawaito a cikin tsauraran matakan tsaro a zaben cike gurbi na zaben Imo, wasu da ake zargin barayin siyasa ne sun tarwatsa tare da kwace akwatin zabe a dakin taro na Umuarusi Amandugba a daidai lokacin da jami’an tsaro suka cika a karamar hukumar Isu ta jihar Imo.
Idan zaku iya tunawa yau ne ake ci gaba da gudanar da zaben gwamna a jihohin Adamawa da Kebbi, da gundumomin sanatoci biyar, da kuma mazabu 31 na majalisar tarayya da na jiha 58.
Vanguard ta wallafa wasu ‘yan baranda kusan biyar ne suka mamaye rumfunan zaben da misalin karfe 09:19 na safe duk da kasancewar jami’an tsaro da yawa.
Daya daga cikin wadanda suka kada kuri’ar mai suna Chibuike, wanda ya yi magana da jaridar da aka ambata a baya ya ce mazauna yankin na fargabar kare lafiyarsu yana mai jaddada cewa an ga motoci masu sulke na jami’an tsaro suna sintiri a yankin kafin a kwace akwatin.
Ya ce: “Muna jin tsoro. Kun ga yadda suka kwace akwatin zabe tare da jami’an tsaro kuma ko da ku aka shirya.
Muna tsoro kuma ba mu da lafiya. Ta yaya za a yi zabe da abin hawa sulke Wannan ba daidai ba ne.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ