Ƴan Sanda Sun Cafke Riƙaƙƙun Ƴan Daba 22 A Dorayi Kano

FB IMG 1709485484086

Rundunar ƴansandan Najeriya, reshen jihar Kano ta tabbatar da kama riƙaƙƙun yan daga 22 da sara da sukan al’umma a unguwar Ɗorayi da ke jihar.

Alfijir labarai ta rawaito matakin ya zo ne sakamakon ɓarkewar faɗa tsakanin ƴan daba a unguwar a jiya Laraba, sanadin da ya kauye ya koma kai harin kan me uwa da wabi, musamman ga Musulmai da ke dawowa daga sallar Asham.

A wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki da Kwamishinan Ƴansanda na jihar, Muhammad Usaini Gumel ya kira a yau Alhamis, ya bayyana cewa rundunar ta kuma ayyana neman wasu yan daba 30 ruwa a jallo. Ya ce yan daga ne da ake zargi da suka addabi Ɗorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale.

A cewar Kwamishinan, duk wani uba da ya zo belin dansa to za a rike shi a matsayin abokin aikata laifin nasa.

Muhammad Usaini Gumel ya kuma bayyana aniyar rundunar ta samar da sabon ofishin yaƙi da ayyukan daba a unguwar ta Ɗorayi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *