Alfijr ta rawaito ‘Yan ta’adda sun kashe hakimin kauyen Mulo da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja, Malam Usman Garba.
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Disamba, 2022, inda suka yi awon gaba da mutane hudu ciki har da hakimin kauyen.
An tattaro Garba an kashe shi ne tazara kadan da kauyen.
An bar gawarsa a baya yayin da ‘yan ta’addar suka tafi tare da sauran mutane ukun.
Kwamishinan tsaron cikin gida na Neja Emmanuel Umar ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin wani taron tsaro da aka gudanar a ranar Juma’a.
Ya ce: “Akwai cigaba a harkar tsaro a jihar.
“An samu raguwar hare-hare amma muna sane da cewa barazanar tana nan.
“A kwanan nan, mun ga hare-hare a yankunan Mashegu, Mariga, da Kontagora.” in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇