Ƙungiyar ƙwadago ta kira taron gaggawa bayan jami’an tsaro sun kai sumame ofisoshin ta

FB IMG 1723228631143

Biyo bayan samamen da jami’an tsaro suka kai shelkwatar ƙungiyar kwadago ta ƙasa NLC, kungiyar ta kira taron gaggawa na kwamitin koli a gobe Asabar.

Alfijir labarai ta ruwaito hakan na zuwa ne a yayin da kungiyar marubuta Ƴan kwadago ta LAWAN ta shiga jerin kungiyoyin dake Alla-Wadai da kai samamen.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar Laraba ne jami’an tsaro suka yi dirar mikiya a ofishin na NLC dake Abuja.

A cewar ƙungiyar, jami’an tsaron sun tafi da wasu takardu da suke zargin da su aka yi amfani wajen tunzura matasa don su fito zanga-zanga.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kungiyar ta shirya taron gaggawa a gobe Asabar da misalin karfe 4 domin daukar mataki kan samamen.

Ana saran taron zai gudana ne ta kafar Internet.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *