Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano Ya Sha Alwashin Kwato Dukiyoyin Al’umma Da Aka Sayar Ba Bisa Ka’ida Ba

Alfijr ta rawaito gwamnatin jihar Kano mai jiran gado karkashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana aniyarsa na kwato kadarorin al’umma da ake zargin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sayar wa ‘yan uwa da Ƴaƴansa.

A cewar Dr. Abdullahi Baffa Bichi, yace an sayar da ofishin hukumar da ke kan titin Jiha a kan kudi naira miliyan 10 ga Abba Ganduje, amma yanzu an crfanar da shi akan sama da Naira miliyan 300.

A wata sanarwa da Dr. Bichi ya raba wa manema labarai a Kano, ya nuna matukar damuwarsa game da abin da gwamnatin mai barin gado ta yi, wanda ya bayyana a matsayin “kamar barna” da barnatar da dukiyoyin jama’a.

Ya kara da cewa gwamnati mai jiran gado za ta binciki duk wata hanya ta doka don kwato kadarorin jama’a da ake zargin an sayar da su.

Ziyarar da kwamitin Dokta Bichi ya kai ofishin kula da harkokin shari’a na daga cikin kokarin gwamnati mai jiran gado na tantance irin barnar da gwamnatin mai barin gado ta yi.

Dakta Bichi ya yi gargadin cewa wasan na gaskiya zai fara ne daga ranar 29 ga watan Mayu da gwamnati mai jiran gado ta karbi ragamar mulki.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *