Wani Likita Ya Yi Wa Mara Lafiya Fyade A Asibiti


Alfijr ta rawaito ana zargin likitan da yi wa mara lafiyar, wadda kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce, allurar kashe kuzari, sannan ya yi mata fyade.

’Yan sanda sun bayyana wa kotu cewa Dokta Ayodele, ya yi wa mara lafiyar, wadda kwararriyar ma’aikaciyar jinya ce, allurar kashe kuzari, sannan ya yi mata fyade.

“A yayin bincike an gano bidiyon fyaden da ya yi, sannan gwajin asibiti ya tabbatar cewa an yi wa wadda ke karar fyade,” in ji takardar cajin da aka gabatar wa kotun.

Dan sanda mai gabatar da kara, Gbenga Ayeni, ya ja hankalin kotun cewa likitan, wanda ya shekara 27 yana aiki, ya aikata laifuka masu girma na fyade da kuma rashin dattaku, don haka ya kamata a tsare shi.

A kan haka ne alkalin kotun majistare, Gbadeyan Jumoke Kamson, ya amince a tsare likitan sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Mayu da muke ciki.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *