Zargin Amfani Da Sauti: Wani Mawaƙi Ya Maka Kafar BBC Hausa a Kotu

BBC Court

Wani mawakin Hausa mai suna Abdul Kamal, ya maka Sashen Hausa na BBC a gaban babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano bisa zargin amfani da kidan wakarsa ta ‘Maryamu’ ba da izininsa ba.

Alfijir Labarai ta rawaito Lauyan mawakin, Barista Bashir Ibrahim Umar ya shaida wa kotun cewa BBC suna amfani da kidan wakar Abdul a shirin su mai suna ‘Daga Bakin Mai Ita’ ba tare da izininsa ba, wanda hakan ke iya janyo masa matsala a harkar sana’arsa.

“Kasancewarsa mawaki mai tasowa, hakan na iya zama matsala gare shi domin wasu za su yi zaton shi ne ya dauki kidan daga BBC don neman shuhura ko wani abu makamancin hakan,” in ji lauyan nasa.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Don haka lauyan ya nemi kotun da ta dakatar da kafar BBC daga ci gaba da amfani da sautin kidan, ya kuma nemi kotun da ta tilasta BBC biyan Abdul Kamal diyyar Naira miliyan 120

Sai dai lauyan BBC, Barista Shakirudden Mosobalage ya mayar da martani cewa BBC ta sayi sautin kidan ne daga hannun wani kamfani da ke zaune a Abuja.

Barista Shakirudden Mosobalage ya kuma roki kotun da ta ba su dama su gabatar mata da wasu takardu, rokon da kotun ta amince da shi.

Alkalin kotun, Mai sharia. N. M. Inusa ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba.

Katsina Daily News

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *