Alfijr ta rawaito Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta ce tana jin takaicin kayen da jam`iyyar NNPP ta yi mata a jihar Kano a zaben gwamnan da ya wuce.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya shaida wa BBC cewa, babban abin bakin ciki shi ne a ce sun rasa Kano.
Ya ce, “ Kamar Kano, a ce mun rasa Kano, to amma laifin wasu ne ya sa muka fadi a Kanon.”
Shugaban na APC, ya ce “ Akwai wadanda ba su yi abin da ya kamata ba, ga shi a yanzu ya sanya ‘ya’yan jam’iyar cikin wani hali saboda nasarar da jam’iyyar ba ta samu ba, bayan ga shi su sun yi duk abin da ya kamata su yi.”
Sanata Abdullahi Adamu, ya ce Kano tana cikin jihohin da suke bugun kirji su ce wannan tamu ce, domin duk abin da za su yi Kano na kan gaba a lissafinsu.
Ya ce, “ Saboda wasu abubuwa na son zuciya an samu a cikin wani hali domin bai kamata a ce mun rasa Kano ba, to amma duk abin da ya samu bawa da sanin Ubangiji.”
“ Sai da muka ja dukkanin gwamnonin jam’iyyar APC a jihohin Najeriya a kan a rage son zuciya tun kafin zabe, kuma muna ganin son zuciyar ne ya ja mana rashin nasara a jiha kamar Kano,” In ji shi.
Shugaban APC ya ce yanzu jira suke duk hayaniyar zabe ta lafa don za su dauki mataki a kan duk wanda ya yi wa jam’iyyar abin da bai dace ba.
Sanata Abdullahi Adamu, ya ce to amma duk da rashin nasara a Kano, suna gode wa Allah da Ya ba su nasara a zaben shugaban kasa da kuma a wasu jihohin.
Ya ce, “ Zaben ma da ake jira za a kammala a Adamawa da Kebbi, mu ne za mu ci in Allah Ya yarda har ma mu je mu yi guda.”
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ
This is a welcome development in respect to Just concluded Gubernatorial election particularly in Kano State. I hoped saboteurs should also be dealt with. We tried all our best, but inshallah victory is ours at the end.
Haka Allah yaso sai dai fatan nasara wani karon, su kuma wadanda suka ja faduwa ayi musu afuwa domin komai nufin Allah bayin kansu bane
Insha Allah zamuci zabe,Amma yakamata aduba zaben House of Representatives na Birninkudu da buji .