Alfijr ta rawaito Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ‘yan Najeriya su zabi wanda suke so daga kowace jam’iyya’ a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Landan.
Shugaban ya kuma ba da tabbacin cewa babu wani dan siyasa da za a bari ya tursasa ‘yan Najeriya.
Da yake magana kan zaben 2023, Buhari ya ce: “Ya kamata ‘yan Najeriya su zabi wanda suke so daga kowace jam’iyya.
Ba za a bar kowa ya tattara kayan aiki da ’yan daba don tsoratar da mutane a kowace mazaba.
Haka nake so in shiga tarihin Nijeriya, a matsayina na shugaba.”
Shugaban ya kuma yi magana kan yiwuwar ci gaba da mulkin APC a 2023; Ya ce: “Mu (APC) za mu ci zabe, Tinubu dan takarar shugaban kasa sanannen dan siyasa ne a kasar nan.
Ya yi gwamna karo na biyu a Lagos.
Ina ganin jam’iyyar ta yi sa’a ta amince da shi ya zama dan takara.”
A watan Fabrairu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin gyaran zabe da aka sake yi a matsayin doka.
Kundin Kudirin Gyaran Zabe na 2022 gyara ne ga Dokar Zaɓe ta 2010.
An rattaba hannu kan kudirin dokar ne domin taimakawa Najeriya inganta harkokin zabe daga na baya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux