Za’a dade ana tunawa da irin gudunmawar da Alh Aminu Dantata ya bayar a duniya – In Ji Sarkin Kano na 15

1000532531

Bayan dawowarsa daga garin Madina dake Kasar Saudia Arabia domin jagorantar jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci iyalan Marigayi Alhaji Aminu Dantata domin yi musu Ta’aziyyar rasuwarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace za’a duniya baki daya bazata manta da irin gudunmawar da Alhaji Aminu Alhasan Dantata ya bayar ba wajen cigaba a fannoni daban daban.

Mai Martaba Sarkin ya jagoranci gabatar da addu’oi na musamman ga marigayin inda yayi addu’ar Allah ya jaddada rahama ga Marigayin ya Kuma bawa iyalansa da al’umar jihar Kano da Kasa da duniya baki daya hakurin jure rashinsa.

Kazalika Mai Martaba Sarkin yakan makamanciyar irin wannan ziyarar Ta’aziyyar ga Hajiya Mariya Dantata inda yayi addu’ar Allah ya gafarta masa ba bashi aljanna madaukakiya.

Kamar kowanne lokaci dai Mai Martaba Sarkin ya samu rakiyar Hakimai da sauran al’uma masoya Sarki tun daga fitowarsa zuwa komawa fadarsa dake gidan Nassarawa a birnin Kano.

Sa hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa Sakataren Yada labarai na Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR JP CNOL.
06/07/2025

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *