Yau ƴan canji za su rufe kasuwar canjin kuɗaɗe a Abuja

IMG 20240111 112459

Kungiyar ƴan kasuwar canji ta Abuja ta ce daga ranar Alhamis za ta rufe kasuwar canji har sai abin da hali ya yi sakamakon tsadar dala da ke ake fama da ita a Najeriya.

Alfijir labarai ta rawaito Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Dauran shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Darajar takardar kudin Najeriya – Naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin gomman shekaru na tarihin kasar.

A kasuwar canji, a ranar Talata, an yi musayar naira kan kowace dala a kan N1,520 yayin da a hukumance ake sayar da dala kan N892 da N910.

Kungiyar ‘yan canji ta alakanta tashin farashin dalar da ayyukan kamfanin da ke hada-hadar kudade ta Intanet irin na Crypto da ake kira Binance

Hakan ne ya sa kungiyar yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta hana ‘yan Najeriya hulda da kamfanin na Binance, idan dai har ana son karyewar farashin dalar.

BBC Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

One Reply to “Yau ƴan canji za su rufe kasuwar canjin kuɗaɗe a Abuja”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *