Yarjejeniyar Da Aka Cimma Yayin Zaman Da Kungiyar Kwadago Da Gwamnatin Tarayya

FB IMG 1717367892511

Ana kyautata zaton nan gaba kadan kungiyar kwadago ta Nigeria ta janye yajin aiki da ta shiga don neman karin mafi karancin albashi.

Kungiyar za ta sanar da matsayar da ta dauka kan karin albashin bayan wata yarjejeniya da cimma da gwamnati a zaman da suka yi a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya jiya litinin.

A safiyar Talata kungiyar ta sanar cewa za ta zauna da rassanta ta ji daga gare su, domin daukar matsaya kan wannan lamari.

Ana kyautata zaton janye yajin aikin ne bayan gwamnati ta amince ta kara mafi karancin albashin ya haura Naira dubu sittin da ta gabatar wa kungiyar kafin zaman.

Bangarorin sun yi ittifaki kan haka ne a zaman sirrin da suka gudanar a daren Litinin da kungiyar ta fara yajin aikin gama gari a fadin Najeriya.

Bayan ganawar bangarorin sun fitar da sanarwar cimma matsaya da cewa, “Shugaban kasa a shirye yake da ya kara mafi karancin albashi daga N60,000.

“Bangarorin za su ci gaba da tattaunawa a kullum na tsawon mako guda domin cimma matsaya kan wannan lamari.

“Kungiyar kwadago za ta je ta tattauna da rassanta kan wannan tayi da gwamnatin ta yi mata, domin cimma matsaya ta sassauta yajin aikin nata.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *