Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Aike Wa Majalisa Karin Sunayen Ministoci

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika karin sunayen mutanen da yake son nadawa ministoci ga Majalisar Dattawa.

Tinubu ya aike wa majalisar sunayen ne a yayin da take tsaka da tantance karashen mutane 28 da ya aike mata da farko a ranar Laraba.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ya mika sunayen ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswil Akpabio.

A makon jiya ne Tinubu ya mika wa majalisar sunayen rukunin farko na mutanen da yake son nadawa ministoci daga 25 daga cikin jihohi 36 da birnin tarayya da ke kasar — saura jihohi 11.

Jihohin da ake jiran sunayensu ne shugaban kasar ya mika sunayen ministocinsu su ne: Kano, Legas, Kebbi, Filato, Adamawa, Zamafara, Gombe, Yobe, Edo, Bayelsa, da kuma Osun.

Mutanen da ya fara bayarwa sun hada da mata bakwai da maza 21, wadanda cikinsu kuma akwai tsoffin gwamnoni hudu; ’yan majalisa masu ci uku, tsoffin ‘yan majalisa uku, hadiman shugaban kasa uku, da shugaban hukumar gwamnati daya.

A jerin sunayen da ya bayar da farko, jihohi biyu, Katsina da Kuros Riba sun samu mutum biyu kowannensu.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

One Reply to “Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Aike Wa Majalisa Karin Sunayen Ministoci”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *