Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 43 da laifin kashe matarsa a Yobe

FB IMG 1703222676383

Rundunar ‘yan sandan ta ce jami’anta na yi wa mutumin tambayoyi domin bayyana al’amuran da suka shafi mutuwar matarsa.

Alfijir labarai ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta ce ta kama wani mutum mai suna Abubakar Musa mai shekaru 43 da haihuwa da laifin mutuwar matarsa Ammi Mamman a Damaturu.

DSP Dungus Abdulkarim, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Juma’a, inda ya ce lamarin ya afku ne a unguwar New Bra-Bra Estate da misalin karfe 4:48 na safiyar ranar Alhamis.

Abdulkarim ya ce wanda ake zargin suna kan gado daya da matar ne a lokacin da aka caka mata wani abu a wuyanta, wanda ya yi sanadin zubar da jini mai yawa wanda ya kai ga mutuwarta.

Ya ce jami’an tsaro na ‘yan sanda suna yi wa mutumin tambayoyi domin bayyana al’amuran da suka shafi mutuwar matarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya yi kira ga duk wanda ke da sahihin bayani kan lamarin da ya fito domin tabbatar da adalci ga wanda ake zargi da kuma wacce ya rasu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *