‘Yan sanda sun ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su, sun damke barayin shanu biyu a Kogi
Best Seller Channel
Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke aiki da sashin Ajaokuta, sun ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa, wanda aka fitar a ranar Litinin kuma aka gabatar da ita ga manema labarai a Lokoja.
Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP William Aya, ya bayyana cewa an ceto mutanen ne a ranar Asabar.
Best Seller Channel
A cikin sanarwar, ya ce, “A ranar 18/12/2021 da misalin karfe 1600 na safe, bayan samun labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun tare hanyar da ke tsakanin NEPA da ASCOL, inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi domin tsoratar da direban motar domin su aikata mugun aikin nasu. .
” A cewarsa, bayan da aka samu labarin, jami’an ‘yan sandan suka yi gaggawar shiga cikin lamarin, inda suka yi taho-mu-gama da ‘yan bindigar, yayin da duk suka tsere zuwa cikin daji, kuma ana cikin haka ne aka ceto mutane biyu ba tare da jikkata ba.
Ya ce ana ci gaba da kokarin ganin an kama ‘yan bindigar.
A wani labarin kuma, jami’an rundunar ‘yan sanda reshen Enjema sun cafke su biyun Mohammed Alhaji da Amadu Sule Juji wadanda suka kware wajen satar shanu a garin Enjema da kewaye.
Ya ce kama shi ya biyo bayan korafe-korafen shanu 15 da suka bace daga sansanin Fulani da ke Okobo.
Best Seller Channel
Rundunar ‘yan sandan ta dauki matakin ne ta hanyar gudanar da ayyukan sirri tare da cafke wadanda ake zargin a Ogboji da ke Unguwar Ankpa tare da kwato shanu 14.
Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu idan an kammala bincike,”
Sanarwar ta fito daga kakakin Yan Sandan jihar kogi
DSP William Aya