Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Usaini Gumel ya ce ba za su bi umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan batun fitar da Sarki Aminu Ado daga gidan sarki na Nasarawa ba.
Alfijir labarai ta ruwaito cewar idan dai za a iya tunawa Gwamna Yusuf a daren ranar Alhamis ta bakin babban mai shari’a na jihar kuma kwamishinan shari’a, Haruna Dederi, ya umurci kwamishina da ya fitar da tsohon Sarkin Kano na 15 daga ƙaramar fadar Nasarawa inda yake zama.
Da yake magana a wata hira da jaridar The Punch ta wayar tarho a ranar Juma’a, kwamishinan ‘yan sandan ya ce bin umarnin gwamnan zai kasance tamkar “haure” ne.
A cewarsa, gwamnatin da ta bada wannan umarni ta shigar da ƙara a babbar kotun jihar kan hukuncin korar da za a yi a ranar Litinin 24 ga watan Yuni 2024.
“Rundunar ‘yan sanda ba za ta kori tsohon sarkin ba, domin ita wannan gwamnati ta shigar da kara a babbar kotun jihar kan hukuncin korar, wanda zai zo a ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.
A halin da ake ciki dai an tsaurara matakan tsaro a kusa da ƙaramar fadar ta Nasarawa inda a halin yanzu sarki Aminu Ado Bayero yake.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj