Majiyar ta ce “Mun tsira da kyar a yau, an kai wa ayarin motocinmu hari ne a tsakanin garin Beneshiekh da Mainok mai tazarar kasa da kilomita 60 zuwa Damaturu
Alfijir Labarai ta rawaito wasu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne sun kai hari kan ayarin motocin Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, inda suka kashe dan sanda daya.
Rahotanni sun ce an kai harin ne a kan ayarin a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Asabar, sannan aka jikkata wasu ’yan sandan su biyu.
Gwamnan na kan hanyarsa ce ta komawa Damaturu bayan ya halarci taron yaye dalibai karo na 24 na Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno.
A cewar wani ganau da ke cikin tawagar da ya nemi a sakaya sunansa, maharan sun bude wuta kan ayarin motocin daga bangarorin biyu na babbar hanyar, inda suka nufi direbobin motar.
Majiyar ta ce “Mun tsira da kyar a yau, an kai wa ayarin motocinmu hari ne a tsakanin garin Beneshiekh da Mainok mai tazarar kasa da kilomita 60 zuwa Damaturu bayan halartar taro karo na 24 na yaye daliban Jami’ar Maiduguri.
“’Yan ta’addan sun bude wuta kan ayarin motocin daga bangarori biyu, inda suka kashe dan sanda guda nan take, yayin da wata majiyar ta ce dayan kuma ya mutu daga baya sakamakon zubar jini da yawa saboda raunukan harsasai.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
“Amma gaskiya mun bar Maiduguri a makare, sai wajen misalin karfe 5:40 na yamma,” in ji shi.
Sai dai Gwamna Buni ba ya cikin ayarin motocin a lokacin da lamarin ya faru kasancewar ya tafi Abuja ne domin gudanar da wani aiki.
Wannan dai shi ne karon farko da aka kai wa ayarin motocin Gwamnan hari tun bayan barkewar rikicin Boko Haram shekaru kusan 13 da suka gabata.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu cikakken bayani kan yawan wadanda aka kashe ko aka jikkata wa su ’yan ta’addan.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp