Wasu Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mahaifiyar Shahararren mwakin nan Dauda Kahutu Rarara.
Rahotanni na nuni da cewa Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.
An yi garkuwa da Hajiya Hakima Adamu ne a gidanta da yankin Kahutu a Karamar Hukumar Danja ta Jihar Katsina.
Shaidu a kauyen sun ce da misalin karfe daya na dare ne dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi awon gaba da ita.
“A kafa suka zo, kuma kasancewar ba su yi harbi ba a lokacin da suka kai harin suka yi garkuwa da ita cikin ’yan mitoci.Dattijuwar ba ta yi musu gardama ba a lokacin da suka ce ta biyo su.
“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, mahaifiyar Rarara kadai suka dauka.
“Babu wani yunkuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda suna dauke da bindigogi,” in ji wani mazaunin kauyen na Kahutu.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj