Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Kai Farmaki Ofishin ‘Yan Sanda Sun Kashe Daya A Katsina

IMG 20240120 061205

Wasu ‘yan bindiga sanye da hijabi sun kai hari ofishin ‘yansanda, tare da kashe dan sanda guda daya a kauyen Saki Jiki da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Alfijir labarai ta rawaito kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abubakar Aliyu Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wani dan sanda ya samu rauni a harin, daya kuma ya rasu.

Ya ce, “A ranar Alhamis da misalin karfe 8 na dare wasu ‘yan bindiga sanye hijabi, suka farmaki ofishin ‘yan sanda da ke kauyen Saki Jiki a Karamar Hukumar Batsari.

“Jami’an sun yi artabu da su kuma sun yi nasarar dakile harin. Sai dai jami’i daya ya rasa ransa sannan wani ya samu rauni sakamakon harin.

Karamar hukumar Batsari dai na fuskantar sabbin hare-haren ‘yan bindiga a baya-bayan nan.

A cikin mako guda, ‘yan bindiga sun kai hari biyu a yankin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *