Yadda ’Yar Shekara 3 Ta Zama Miloniya Daga Zuwa Sayen Burodi

Masu iya magana sun ce ‘Dare daya Allah kan yi Bature”
kamar yadda hakan ta faru ga wata ’yar karamar yarinya da ta je sayen burodi kuma hotonta da aka dauka ya sauya rayuwarta da na iyayenta.

Alfijir Labarai ta rawaito lamarin ya faru ne a kasar Afirka ta Kudu ga yarinyar mai shekara uku mai suna Lethukhanya Mjaja da iyayenta suka aike ta sayo burodi, bayan ta sayo a hanyarta ta dawowa gida sai ta tsaya ta shiga cikin wani ruwa da ke kwanciya a kan hanya tana wasa.

Sai wani kawunta mai sana’ar daukar hoto ya gan ta, kuma cikin wasa ya dauki hotonta rike da burodi tana dariyar wasan da yake yi mata, ya kuma sa a shafinsa na Intanet.

Kafin a ce kwabo, sai hoton ya yi farin jini inda aka riqa yada shi a shafukan sada zumunta na kasar.

Abin ya faranta wa kamfanin burodin rai, inda a cewar wani rahoto, bayan da suka yi amfani da hotonta a manyan allunan talla da kuma motocinsu na sayar da burodi hakan ya kara musu farin jini da kasuwa, don haka sai suka yanke shawarar yin kyauta ta musamman ga yarinyar da iyayenta.

Sun nemi iyayen yarinyar da mai hoton da kuma yarinya suka musu kyauta mai tsoka na makudan kudin yin hoton yarinyar nan a manyan allunan talla na kasar.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *