Kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP Dr Umar Ardo, ya shigar kan zaben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.
Alfijir labarai ta rawaito Ardo ya garzaya kotun kolin ne yana neman ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa,wanda kotun daukaka kara ta tabbatar.
Wanda ya shigar da kara ya bukaci kotun ta soke zaben da ya ayyana Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa saboda rashin bin dokar zabe.
Kotun daukaka kara dai ta yanke hukuncin korar karar ne,inda tace wadanda suka shigar da karar ba su tabbatar da zargin almundahana da rashin bin dokar zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi ba.
Kuma bayan amsa tambayoyin da lauyan me karar yayi, Alkalin kotun Mai shari’a Okoro ya yi watsi da karar, sannan ya tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta Yanke akan Shari’ar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl
