Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da kwamatin wocin gadi da zai fito da bukatun Najeriya yayin babban taron duniya, kan sauyi yanayi na 2023 COP28 wanda za a gudanar a hadaddiyar daular larabawa a tsakanin 30 ga wannan watan zuwa 12 ga watan gobe na Disamba.
Alfijir Labarai ta rawaito lokacin daya ke kaddamar da `yan kwamatin a Abuja, mataimakin shugaban kasan yace yana daga cikin alhakin dake kan yan kwamatin samar da wata taswirar da zata kai ga Najeriya cin gajiyar taron musamman kirkiro da dabarun adana makamashi.
Sanata Kashim Shettima yace ya zama wajibi Najeriya ta kimtsa sosai gabannin taron domin tabbatar da ganin cewa dukkan burikan kasar a game da kaucewa kalubalen sauyin yanayi sun kai ga cika.
Yace zai zama abun kunya wakilan Najeriya a wajen taron su gaza dawowa da fa`idojin dake tattare da wannan mahimmin taro na COP28 wanda zai taimaka wajen fito da wasu sabbin dabarun adana makamashi.
Yace Najeriya na dakon tallafin kasashe da masu saka jari da zasu shigo kasar domin kulla yarjejniyar samar da batira masu adana makamashi.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
A jawabin sa shugaban kwamatin kuma ministan Muhalli na tarayyar Najeriya Alhaji Balarabe Abbas Lawan, ya tabbatar da cewa kwamatin nasu zai nazarci kundin bayanan taron da nufin zakulo wasu mahimman fasahohin zamani da suka hada da samar da batiran adana wuta wanda da zasu kawo karshen matsalolin karancin wuta a Najeriya.
“Da man dai babban abun da muke son yi, shine tabbatar da ganin annobar yawan katsewar wutan lantarki a Najeriya ya kau, abun da zamuyi kokarin samar shine wani runbu adana makamashi wanda ke da kamanceceniya da abun da ake kira UPS wanda da zarar an dauke wuta shi kuma zai cigaba da bada haske, a takaice dai baza a sake samun daukewar wuta ba”
CRI Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp